Wani dan india yana bautawa Donal Trump


  

Mutumin mai suna Bussa Krishna yanada shekara 31 kuma haifafen kasar india ne.

Bussa krishna yana zaune ne a wani kauye Telengana dake kasar india. Bussa Krishna a baya dan addinin hindu ne amma tun shekara 3 da suka wuce ya fara bautar hoton shugaban kasar amurka Donal Trump.

Bussa ya bayyana manema labarai cewa ya yanke shawarar bautar ne saboda kaunarsa ga Trump. Yace " Na yarda cewa
mu mutanen kasar india munada karfi sosai a harkar bauta kuma zamu iya ta hanyar so kadai zaka iya nasara ga kowa.

Yakuma kara da cewa " Ta hanyar So kadai zamu iya nunawa kasar amurka irin kaunarmu garesu. Ya kuma ce yanada yakinin zai magance masa duk matsalarsa in ya rokeshi kuma yana fatan bautar tasa zata isa ga Trump.

Bussa ya ajiye hoton Donal Trump ne a wani kebebben wuri a dakinsa kuma yana bauta masa ne da fulawa mai kamshi. Bussa yana bautar ne sau 5 a kowacce rana kuma kamar kowanne addini shima yanada kaidodin daya sanyawa kansa.



Mazauna kauyen Telengana sunyita takaddama da shi bussa suna fadi masa yaje a duba lafiyar kwakwalwa amma shi ya dage cewa lafiyarsa kalau don haka ba inda zaije.

Labarin Bussa yayita yawo a kafafen sada zumunta na kasar india saidai haryanzu baa jiyo Ubangijin nasa wato Shugaba Donal Trump yace wani abu kan lamarin ba.