Karanta cikaken bayaninda yayi musu kafin su koma APC.
A irin wannan lokaci da aka samu ficewar wasu manyan 'yan siyasa daga jam'iyyar APC zuwa PDP wasu jaridu sunyi kokari wajen waiwayen gargadinda tshohon shugaban kasa GOODLUCK JONATHAN yayiwa 'ya'yan jam'iyyar PDP a shakarar 2015 tun kafin su sauya sheka zuwa APC.
A lokacinda akasarin 'yan jamiyyar ta PDP sukaita barin jamiiyyar saboda tasha kaye a zaben 2015 sai Jonathan ya sanarda wani gargadi ga masu fitar.
Yace " A irin wannan lokaci da muka rasa nasara a zabe yakamata kowanne dan jam'iyya ya fahimci cewa akwai haka a siyasa ya tsaya a gidansa ina gargadinku karku fice daga PDP kuje APC don cimma muradan kanku.
" Har yanzu PDP ce jamiyyarda zata baka takara bisa chanchantarka.
Jonathan yakara da cewa "Ina shawartarku 'yan uwa ku zauna a jam'iyyarku mai inganci karku fita wai don tunanin APC zata cika muku cikinku. Na tabbata ko kun fita zaku dawo PDP da yunwa ajikinku.
Gashi dai zancen ya tabbata sun fita kuna sun dawo din saidai ba'asan ya zata kaya ba a zaben dake tafe na 2019 ko senatocin duka zasu koma kujerarsu.

