Ibrahim Coomasi jajirtaccen mutum ne kuma dan kishin kasa.
Tshohon shugaban yan sanda Alh. Ibrahim Coomasi ya rasu ne a asibitin Orthopaedic Hospital, Katsina da karfe 6pm ayau alhamis.
Ibrahim coomasi ya kasance d'a ne ga babban dan kasuwa kuma mai bada ilimi a shekarun baya wato Mallam Ahmadu Coomasi wanda ya rike sakatare na yankin arewa.
An haifi Ibrahim Coomassie ne a garin Katsina a ranar 18 March 1942. Yayi karatu ne a Provincial Secondary School, Zaria, Barewa College, Zaria, Detective Training College, Wakefield, UK.
Ya rasu yabar 'ya'ya 6 da mata guda 1, sannan kuma yarasu ne yanada shekara 76 a duniya.
Yayi aiki ne tun daga shekarar 1993 zuwa 1999 a karkashin mulkin genaral abacha.
Masu sauraron kafafen labarai sanannen mutum ne garesu saboda yadda yake yawan gwagwarmaya da kuma sharhi kan siyasa da al amuran yau da kullum.
Allah yagafarta masa.

