Mutane 3 sun rasa ransu a take sa'annan kuma dayawa sun jikkata sakamakon raunuka.
Wani shaidar gani da ido ya bayyanawa manema labarai cewa jirgin yayi hatsari ne alokacin matukin jirgin ke kokarin sauya hanya.
Mutumin yakara da cewa "Saida muka gargadi Driver kada ya juya a lokacin amma sai bai yarda ba jirgin kuwa ya kubuce masa har mutanenda ke rike da jirgin suka fado 3 daga cikinsu sun mutun a take.
Jerry oche shine shubaban NIGERAN RAILWAY COOPERATION ya bayyanawa manema labarai cewa hatsarin ya auku ne bada son mai tukin ba.
A bangaren jami'an yan sanda suma sun tabbatarda aukuwar lamarin inda suka shaidawa majiyar labarai cewa abin ya faru ne a safiyar yau karfe 9:30am.
Tuni akayi gaggawar wucewq da wadanda suka samu raunuka zuwa asibiti domin kulawa dasu.

