mrs Kemi Adesun akan takardar bogi ta NYSC.
Minista Kemi ta kammala digirin farko ne a ranar 11 july 1989 lokacin tana shekara 22 da haihuwaa. Saidai abinda ya tabbatarda takardar NYSC ta bogi ce shine an rubuta tayi bautar kasar ne a shekarar 2009 lokacin tana shekara 30 kuma wanda hakan ya sabawa dokar hukumar ta NYSC wacce ta bayarda dama ne kadai ga wanda baikai shekara 30 ba.
GA HOTON TAKARDAR
A jiki takardar an rubuta YUSUF BOMAI tsohon shugabar kungiyar kuma birigedia sna sojoji matsayin shine yasa hannu. Saidai kuma shi YUSUF BOMAI ya bar aiki a hukumar ne a watan January 2009 ita kuma takardar anyita ne watanni bayan ya sauka.
idan baku manta ba acikin satinnan ne lanarin ya faru kuma cikin masu caccakar abun harda wasu manyan jamiyyar adawa PDP.
'Yan nigeria dayawa sun harzuka akan wannana lamari har wasu nata kira kirayen sauke minitar akan mukaminta saboda yaudarar gomnati datayi.
Har yanzu dai gomnatin nigeria bata ce uffan ba akan wannan badaka ta ministan kudi.


