Uwargidan shugaban majlisar dattawan Nigeria Toyin Saraki ta bayyana cewa mijinta Sen. Bakola Saraki bashida wata alaka da abinda ake zarginsa.
Toyin saraki a shafinta na twitter tace " Anyi amfani da 'yan sanda ne kawai don a hana maigidanta fita daga jam'iyyar APC amma suma kansu sun sani siyasa ce ake masa. Taya zamu dauki nauyin fashi me muke nema a duniya da zamuyi fashi?
Ana zargin Sen. Saraki ne da hannu a wani fashi da akayi a wani banki a garin offa dake jihar kwara wanda 'yan fashin da aka kama suka ambaci sunansa matsayin mai daukar nauyinsu.
Saraki ya musa hakan amma jamian yan sanda basu yarda da kalaman nasa ba har takai sun tura masa gayyata kusan sau biyu bai halarta ba.
Masu sharhi suna kmr akwai lauje cikin nadi a zargin Sarakin saidai a daya bangaren musamman magoya bayan shugaba buhari suna ganin Sarakin baida gaskia shiyasa yaki zuwa.

