Ana zargin dan wasan Super Eagle din ne da dukan matarsa sumayya akan kiran waya.
Majiya ta ruwaito cewa dan wasan yatafi hutu ne sokoto tareda iyalan nasa tun bayan kammala gasar kofin duniya da suka buga, kuma acan ne abin yafaru tsakaninsa da matarsa sumayya.
Ya shigo daki ne ya samu matar tasa tana waya ya fizge wayar daga hannunta abinda yayi sanadin fada tsakaninsu.
Hotunan matar tasa yayita yawo a kafafen sadarwa musamman #Instagram.
Rohotanni kuma sun bayyana iyalan dan wasan sunyi kiran zama na gaggawa domin shawo kan matsalar data auku tsakanin ma'auratan.
Abdullahi Shehu dan wasa ne mai buga kwallon tsakiyar fili (Midfielder), kuma dan wasan kasa da kasa ne. Ya Auri Sumayya ne auren soyayya a shekarar 2015.

