Wannan yaro dan kasar Australia shine mafi girman jiki acikin yara masu irin shekarunsa a duniya.
Likitoci sun bayyana irin hatsarinda wannan yaro yake ciki saboda kankantar shekarunsa.
Tun yanada shekaru 6 a duniya nauyinsa yakai kimanin 100kg wannan yasa alokacinda yakai shekara 7 yakai wani matsayi da likitoci suke cewa (BMI) wanda duk wanda yakai wannan matsayi kiba tana iya hanashi gudanarda wasu abubuwan rayuwa.
A yanzu haka yaron yanada nauyi kimanin 170kg wanda yakai adadin nauyin buhun gishiri uku da rabi.
Wani rahoto da wata jaridar kasar Australia ta fitar ya nuna cewa kusan kashi daya cikin ukun yaran dake yankin Queensland a kasar suna fama da wannan lalura ta kibar jiki.