Labarin Jamila Nagudu tareda santalelen d'anta

Jamila Umar Nagudu fitacciyar jaruma ce data dade ana damawa daita a masana'antar fina finan Hausa.

Jaruma ce wacce take taka rawa a fina finai dayawa kamar. Soyayya, Zaman Aure, ko Ban Dariya. Wasu ma suna ganin itace jaruma guda da baa taba kawo mata wani Fim ta gagara taka rawa ba duk wahlarsa.

Masoyan Jamila sunata tambaya ko ta taba aure? Kuma taushe ne har haifi wannan santalelen saurayi?

Jamila bada amsa cewa ita haifafiyar bauchi ce a wani gari da ake kira gumau acikin Taura local LGA amma ta girma ne a bauchi tayi karatu har tayi aure ta haifi wannan yaro daga bisani kaddara  ta auku suka rabu da mijinta sai ta koma kano ta shiga harkar fina finai.

Wannan yaro yagirma ne a hannun mahaifinsa shiyasa ba kowa yasan tanadashi ba sai wadanda ke kusa daita.

Ta Kuma bayyana har yanzu tanada niyyar yin wani auren domin samun karuwar zuriarta.