Na samu daukaka alokacinda nakeda kuruciyata komai yana tafiya daidai banida matsala a wancan lokacin. Na samu shahara da ba kowacce mace ta samu ba a fim din Hausa. Kwatsam! Sai kaddara tazo kaina babu zato ba tsammani babu ta rabani da abokaina, Abokan aikina sannan ta rabani da masoyana wadanda sune sirrin daukakata. Tabbas babu wanda bazaiyi mamaki dusashewar haskena a duniyar fina finai ba koda kuwa baya kaunata saidai kuma ba'a mamaki da hukuncin ubangiji.
Rayuwata ta koma kamar bani bace ake rububi da soyayya koina aka ambaci sunana sai kaga masoyana sun amsa amma sai gashi nadawo abar Allah sarki andaina jin ko labarina bare in samu sanyin soyayyar masoyana ko zanji sanyi arayuwata.
Watakila faruwar haka ne kaddarata kuma babu wanda yawuce mukaddarin ubangiji.
Ni kaina bazan iya tuna abinda ya faru dani ba kuma bansan meyasa haka ta faru dani babu wanda nake zargi da zama silar abinda ya faru dani. Abinda zuciyata take fadi ayanzu shine taya zan samu mafita tunda na farka daga baccinda nayi a baya. Allah kadaine yasan dalilin faruwar haka gareni kuma shi nake roko idan laifina ne silar wannan lamari ya Allah kayafemin idan kuma wani ne silar haka gareni ya Allah kayafe masa ka shirya mu akan tafarkin gaskia.
A irin wannan lokaci yazama dole in godewa yayana Adam A Zango wanda ya tsaya tsayin daka akaina lokacinda babu wani da yaragemin kuma babu wanda keson zuwa inda nake. Adam A Zango shine komai nawa a yanzu dalilinsa ne ma har kuka san halinda nashiga kuma gashi cikin ikon Allah na fita.
A karshe ina rokon duk wanda na taba batawa rai ko kuma nayiwa laifi yayafemin. Na tuba! Masoyana kuma ina godiya gareku da masu min fatan alkhairi harda masu muzantani duka ina kaunarku.
Jarumarku akoyaushe,
Zainab Abdullahi Indomie.