Rahotanni dake fitowa daga shafuka watsa labarai sun bayyana cewa shugaban sabuwar APC injiniya buba Galadima ya gamu da hatsarin mota akan hanyarsa ta dawowa abuja daga jihar Yobe inda yaje ziyara da kuma taaziyya.
Buba galadima tareda dansa guda daya da kuma wasu abokan tafiyarsu hatsarin ya ritsa dasu.
An tabbatarda babu asarar rai a hatsarin saidai wata majiya mai karfi ta tabbatar mana da an dauke mutanen dukansu zuwa birnin kano domin duba lafiyarsu.

