Labari da dumi-dumi: Anyi garkuwa da senata Dino Melaye


Rahotanni sun bayyana anyi garkuwa da senata mai wakiltar kogi ta arewa Dino Melaye. 

Labarin ya fito ne daga wurin senata Ben Murray-Bruce wanda ya rubuta a shafinsa na twitter cewa "Na samu labari cewa wasu yan bindiga sunyi garkuwa da Senata Dino Melaye akan haryarsa ta zuwa kotu kuma kaninsa Moses Melaye ne ya shaidamin. 

Ga bayanin a turance:
A jiya ne wata kotu a abuja ta bayarda belin senata Dino akan kudi naira milyan 5.

A yau kuma yau ne dama ake tunanin senata Dino Melaye zai amsa gayyatar wata  kotu a jiharsa ta Kogi domin a cigaba da shariar da ake wacce ake zarginsa da akan wasu laifuka kusan biyar. 

Har yanzu baa samu labarin inda senata Dino yake ba. 

Sourse: Vanguard Newspaper