LABARAN YAU: Kotu ta wanke Bakola Saraki


Wata babbar kotu a nigeria (supreme court) dake abuja ta wanke shugaban majilasar dattawa BAKOLA SARAKI wanda ake zargi da bayyana kadarorin bogi a lokacinda wani bincike ya biyo kansa.

Mai sharia justice centus nweze shine ya jagoranci yanke hukuncin, inda ya bayyana cewa dukkan laifi da ake zargin SARAKI sharri ne kawai da bita da kulli irin na siyasa. Ya kuma kara da cewa daga yanzu babu wani sauran laifi da SARAKI zai amsa a gaban kotun dukkan laifuka 3 shiri ne kuma an warware don haka babu bukatar cigaba da tuhumar SARAKI akan wadannan.

Sen Bakola Saraki wanda ya fito daga jihar kogi state, dama can ya dade da musa zargin da ake masa akan wannan lamari ya kuma sha fadar cewa sharri ne ake masa.

 HAUSA LINE NEWS: