Alao, shine saurayin marigayiya Aisha adenike diyar tsohon mataimakin gomnan ondo wanda yakasheta a dakinsa a satin daya gabata.
Alao, Wanda yake hannun jamian yan sanda yace "banyi niyyar kashe budurwata ba azahirin gaskia ina kaunarta saidai ta yaudareni alokacinda na fita na barta a daki dawowata keda wuya na sameta da samari a dakina tana soyayya da da daga cikinsu.
Alao ya kara da cewa "kwana shida kenan ina tare da gawar a dakina kuma har na tona kabari acikin dakin don binne gawar masoyiyar tawa.
An ruwaito cewa masoyan biyu sun shafe shekara 5 suna soyayya saidai kuma Alao ya kashe masoyiyar tasa sakamakon kishi da kuma fushi sanadiyyar yaudararsa datayi. Ya kuma karyata zarginda ake yadawa cewa yakashe budurwar ne saboda yayi tsafi da ita.
Aisha Adenike dai dalibace a jamiar Ajasin University dake ondo kuma a bana ne ake sa ran zata kammala digiri na farko a jamiar.
Kwamishinan 'yan sandar jihar ya bayyawa manema labarai cewa suna cigaba da bincike akan lamarin kuma duk wanda yakeda alaka da kisan zasu kamoshi sannan ya kara da cewa saurayin yana yana gabda fuskantar hukunci agaban kotu.