- Duk da cewa tawagar Nijeriya bata kai ga tsallakewa zuwa zagaye na biyu a gasar kofin duniya na bana, Ahmed Musa na neman daga martabar tawagar da kwallon da yaci
Wasan su na biyu a rukuni super eagles ta doke Iceland da ci biyu da nema kuma Ahmed Musa ya zura kwallayen a ragar abokan adawar su
Kwallo na biyu da yaci ta fito takarar jerin kwallo mafi birgewa a gasar kofin duniya ta FIFA na wannan shekarar
Dan Nijeriyan zai yi takara da jaruman yan kwallo da suka taka rawar gani a gasar wannan shekarar
Cikin yan wasa zasu fafata da dan Nijeriya wajen samun kyautar FIFA akwai, Cristiano Ronaldo, Lionel Messi, Courtinho, Lingard, Pavard, Chadli, Modric, Di maria, Quaresma, Quintero da Dzyuba da Cherychev
Ana zaben wanda ya cancanci samun wannan kyuatar a shafin FIFA kafin ranar 23 ga watan Yuli.
Source via: Pulsenews hausa

