Karanta cikaken labarin taimakonta ga marasa lafiya da kuma kananan yara.
Mansura Isah tsohuwar jarumar fina finan Hausa ce kuma uwargida ga shahararen dan wasan Hausa da Turanci SANI MUSA DANJA.
Mansuravta sadaukarda lokacinta ga taimakon jamaa musamman nakasassu da kuma masu karamin karfi ta hanyar samarda wani katafariyar gidauniya mai suna "Gidauniyar taimakon rayuwar yau" wacce a turance ake kiranta da "Today's Life Foundation".
Dukda kasancewar Mansurah Isah matar aure amma hakan bai hanata fita lungu da sakon kauye da birni ba don tallafawa mutane.
Ko a cikin satinnan ta taimakawa wani almajiri mai aikin "shoe shiner" dalilinta saboda yadda ta tausaya masa irin rigar jikinsa da kuma karanci shekaru har ta bashi jarin naira N5000 don ganin kokarinsa na musanya sanaar gyaran takalmin akan yaje barar abinci.
Tallafawa marasa lafiya abune sananne da takeyi duk mai bibiyarta a shafin sadarwa yasan yadda take nemo masu gagararrun cututtaka don nema musu taimako a wurin bayin Allah.
Tana ziyartar mata masu haihuwa don tallafa musu.
Tana ziyarar kauyuka don tallafawa yara su shiga makaranta.
Fatanmu shine Allah ya kara mana masu taimakon acikin alummarmu ta nigeria.





