Jami'an yan sandar fikira sun bukaci Saraki ya mayarda amsar tambayoyinda aka aika masa


Shugaban 'yan sandar nigeria Ibrahim Idriss ya bayyana suna bukatar Sen. Bakoka Saraki ya aikewa Jami'an yan sandar fikira da amsoshin tambayoyinda akai masa.

Acikin wasikarda aka aikawa SARAKI jiya 23/8 an bukaci ya bayyana a gaban kotu yau 24/8 domin amsa wasu tambayoyi don  da zasu baiwa jamian tsaro damar karin bincike.

A kwanakin baya ne aka fara takun sakar tsakanin yandar da shugaban majalisar dattawa Bakola Saraki akan zarginsa da ake na daukar nauyin wasu bata gari 'yan fashi da suka fasa wani banki dake garin Offa a jihar kwara da Sarakin ya fito.

Masu sharhi dai na ganin yakamata Saraki yaje ya amsa tambayoyin saboda fitarda kansa da kuma dumbin yan kasa da suke sa ido kan lamarin.

Tun a baya dai Sen.Saraki ya musa zargin kuma alakantashi da wani yunkuri na dakusarda kaifin siyasarshi don muzantashi a idon duniya.