A lokacinda yake zantawa da jaridar #FinancialTimes Dangote yace shekaru sun tafi domin kuwa shekara 60 ba wasa ba amma hakan bazai hanashi neman sabon aure ba.
Dangote wanda shine shugaban gamayyar kamfin DANGOTE GROUPS. ya taba sakin mata biyu arayuwarsa kuma ya haifi 'ya'ya mata 3 ne duka a duniya.
Dangote ya kara da cewa gaskia yanada karancin lokaci sosai saboda yadda yake gudanarda harkokin kamfanunuwansa kuma akalla yana karbar kiran waya sama da 100 a kowacce rana.

