Dan wasan kungiyar Super Eagle Ahmed Musa ya fadi hakan ne alokacinda suke zantawa da manema labarai.
Ahmed Musa yace "mutane dayawa 'yan kasata sun daukeni wani gwarzo wanda zai cire musu kitse a wuta don haka nima bazanyi kasa gwiwa ba yazama dole inyi kokari don ganin ina samar musu nutsuwa a duk wasanda za'a buga tsakain kasar tawa nigeria dama kowacce kasa.
Ya kara da cewa "Ina kwatanta kaina da manyan 'yan wasa na duniya domin duk kalar wasan ai daya ne banbancin kawai shine samun nasara a kwallo. Shiyasa nake kwarmtanta kaina da CRIASTIANO RONALDO.
Ahmed Musa dai sanannen dan wasa ne wanda yakai matakin kasa da kasa. Yana buga wasa ne a kungiyar
leicestercity
kuma ko a wasan da nigeria ta buga a world cup shine dai zakara da yafi kowanne dan wasa kokari awajen wasanni.