HARAMUN NE KARUWANCI HAR ABADA -Martanin Dr Ahmad Gumi

Martanin ya fito ne bayan wata magana da ake ta yadawa cewa malamin yace mace zata iya karuwanci don cin abinci ko dogaro da kai. 

Shahraren malamin Dr. Ahmad Gumi ya bayyana hakan ne acikin wani karatu da yayi jiya asabar a masallacin Sultan Bello dake kaduna. 

Dr. Ahmad Gumi yace "baya yiwuwa ayi gyara da barna duk tsananin da bawa yashiga dole ne gareshi kiyaye hakkin ubangiji. Musamman mace kiyaye mutuncinta shine babbar ibada gareta kamar yadda yazo Maryam mahaifiyar Annabi isa ta kiyaye mutunci sai Allah ya daga darajarta akan duk matan duniya. 

Dr. Yakara da cewa "Bazai yiwu in fadi wannan magana ba kuma malamai basu fadi haka ba.

Da aka tambayeshi akan masu rubuta wannan maganganu akansa sai yace " Ai dama zaa iya samun haka kamar yadda muke fadin cewa abi sunnah a samu daidaito to akwai wadanda basu son hakan kaga kuwa dole zasuyita yada irin wadannan karairayi don nuna batanci ga masu fada musu gaskia. 

Dr. Ahmad Gumi ya shahara wajen fitarda fatawoyi musamman abinda ya shafi FIQH saidai malamin yana fuskantar kalubale dayawa a wasu fatawoyin da kuma shaanin siyasa daya saba sukar shugaba buhari akai. Wannan yasa dayawa mutane suna ganin sukar buharin ne ma yaja ake yawan muzantashi a hotuna da rubuce rubuce a shafukan sada zumunta.