Gomnati na kokarin sasantawa da Kwankwaso


A ruwaito cewa anga Sen. Rabiu Musa Kwankwaso ya jagoranci wasu sanatoci suna ganawa da Buhari a fadar gomnati Villa dake Abuja.

Ganawar ta biyo bayan wata ganawa da akayi tsakanin Bakola Saraki, Yakubu Dogara, Yemi Osinbajo da kuma shi kansa Shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma duk tattaunar kan batu daya ne na zargin shirin ficewa daga jam'iyyar.


Sen. Rabiu Kwankwaso yana daya daga cikin wadanda ake tunanin zasu fice daga jamiyyar APC sakamon fada da har yanzu suke tsakaninsa da Gomnan jiharsa.

Har yanzu ba'a bayyana makasudin ganawarda Buharin yayi da Kwankwaso ba saidai ana tunanin bazai wuce kan yunkurinda Gomnatin keyi na dakatarda 'ya'yan jamiiyyar APC daga ficewa da suke kanyi ba.