Dalilinda yasa zan bar APC


A yau ranar laraba 4 ga watan july, 2018 shugaban darikar kwankwasiyya kuma senatan tsakiya a jihar kano Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da shugaban jamiyyar PDP sabuwa wato Hon. 
Kawu baraje.

Kwankwaso tareda dumbin magoya bayansa ciki harda yan majilissun jihohi dana tarayya sun gana da kawun barajen ne don tattaunawa gameda yunkurinsu na dawowa jamiyyar idan har tattaunawar tasu ta samu daidaito.

Wani matashi kuma daya daga cikin jigon tafiyar kwankwasiyya ya bayyana dalilin jagoran nasu na barin jamiyyar APC mai mulki.
" Zamu bar APC ne ba don komai ba sai don rashin shugabanci daya addabi jamiyyar tun bayan kafa mulkinta a nigeria. Kowa dai yasan baa tafiya daidai saida jagoranci don haka bazamu bari a rinka cin zarafin kowane dan jamiiyya ba kamar yadda yake faruwa a yanzu, kuma idan Allah yayarda zamu bayyana ranarda Zamu fice daga APC matukar mun samu kyakyawar fahimta da masu fada aji na jamiiyar PDP. Inji wani jagoran kwankwasiyya.

Ko a makonda yagabata sen. Rabiu kwankwaso ya kai ziyara jihar Ekiti don ganawa da gomnan jihar akan batun komawarsa jamiiyar ta PDP.

Jamiiyar APc dai na fiskantar kalubale ne mai girma a wannan lokaci da zabe ke 
karatowa a nigeria wanda hakan yaketa haifar mata da rikici a tsakanin manyan 'ya'yan jamiiyar kamarsu Kakakin majalisar dattawa BAKOLA SARAKI da sauransu.