Buhari ya nada SAS daraktan kamfen nashi a 2019


Rahotanni dake fitowa daga fadar shugaban kasa an bayyana Sen. Ali Modu Sheriff matsayin daraktan kamfen na Buhari a zaben 2019.

A baya bayan nan ne Ali Modu Sheriff yayi sauyin sheka zuwa jamiyyar APC bayan yabar mukaminsa na shugancin jamiiyyar PDP mai adawa.

Bayanin ya fito ne daga hannun mai bawa  shugaban kasa shawara a sha'anin siyasa Gideon Shammani.

Kwamitin da ya kuma nada mawaki DAUDA KAHUTU RARARA matsayin daraktan yada wakokin buhari sannan ya nada jarumin fina finan Nollywood Hon. Desmond Elliot matsayin sakataren yada al'amuran dasuja shafi tallata buhari.

Kwamitin da sukayi nadin sun hada da mataimakin shugaban kasa Profs. Yemi Osinbajo da sakataren gomnatin BOSS MUSTAPHA da Bola Ahmed Tinubu da kuma Mamman Daura.

Kwamitin yace sunyi nadin ne saboda cancantar mutanen da kuma kara karfi ga jamaa masu marawa Buhari baya don samun nasara a zabenda ke karatowa na 2019.