Sheikh Abdush shakur kurd, ya kasance daya ne daga cikin manyan malaman sunnah a kasar iran wacce kasa ce da take cike da al'uma dayawa kuma kasace mai karfin tattalin arziki a kasashen larabawa saidai kuma mulkin kasar yana hannun musulmi mabiya akidar 'shi'a da sune mafi yawa a kasar.
Kafin kashe malamin yasha fama da gwagwarmawa da kira akan bin sunnah wanda hakan yasa ya fuskanci barazana mai yawa a rayuwarsa sakamakon wannan akida tashi data sabawa masu fada aji a kasar.
Ana zargin jami'an leken asirin kasar ne suka hallaka malamin har lahira.
Shekara 25 da suka wuce haka shima mahaifinsa Sheikh abdussatar albulushy an kasheshi wanda shima limamin sunnah ne a yankin bulushistan kuma shima kisan gilla aka masa kamar haka kazalika shima duk an kashesu ne akan wannan akida ta sunni.
Har yanzu dai baaji kasar iran ta mayarda martani kan wannan kisa ba wanda hakan kamar wani nuni ne cewa tana goyon bayan aika aikar.


