An kama mota dauke da harsasai 200,00 a jihar Niger

Hukumar yaki da 'yan fasa kwauri (Customs) ta kama babbar mota dauke da bindigogi da harsasai wanda yawansu yakai 200,000, a jihar niger iyaka da coutonou dake kasar Benin.

Hukumar tace an kama makaman ne a babbar mota da wani maisuna BAKARI DAUDA yake tuka motar zuwa cikin kasarnan.

BAKARI DAUDA ya bayyana cewa baisan cewa makamai bane kayan da aka bashi dakonsu. Ya kuma kara da cewa kayan duka mallakin wani ne mai suna Mr. Martins Anokwara.

Tuni dai jamian suka kama Mr. Martins kuma shima bai musa mallakar makaman ba saidai yace ya sayo kayan ne a hannun wani dilan makamai a kasar kwatanou. Ya kuma kara da cewa ya sayo kayan ne kawai don sayar dasu ga maharba a onitsha.

Shugaban hukumar a jihahin Niger da kwara, Benjamin Binga shine ya bada umarnin kama motar a lokacinda jamian suka bincika motar.

Via:Naijanews.com