An kama dalibai 2 da laifin shiga kungiyar asiri


Makarantar Illorin Polytechnic dake offa, a jihar kwara ta kori dalibai 2 bisa laifin shiga kingiyar asiri.

An kama Daliban ne Tajudden Salem da Temitope Omotosho bisa laifin shiga kungiyar asiri.

A cewar daliban makarantar sun kama shugabannin nasu dumu dumu a cikin ayyukan kungiyar asiri wanda hakan bazarana ne ga zaman lafiya da kuma rayuwar dalibai aduk inda suke.

Shugaban makarantar (Rector) lateef Admola Olagunji, ya bayyanawa manema labarai cewa tuni sun mika daliban ga jamian 'yan sanda don gudanarda bincike kafin a mika su ga koto don zartarda hukunci. Ya kara da cewa dukkan daliban biyu an dakatar dasu daga karatu a makarantar.

An kuma gano cewa masu laifin sunada alaka da wani da suka ambaci sunansa Adewusi Vincent, wanda tun shekarar 2017 aka koreshi a makarantar bisa karancin kwazonsa a karatu.

Shugaban makaratar ya kuma gargadi daliban da su gujewa ayyukan da suka sabawa dokokin makarantar kamarsu. Kungiyar Asiri, Lalata da mata, da kuma ayyukan ta'addanci.

Makarantar Illorin Polytechnic tayi kaurin suna wajen irin wadannan ayyuka na kungiyar asiri saidai an ruwaito cewa an samu raguwar aikin tun bayan samun sabon shugaban makarantar a shekarar 2017.

Via: Vanguard newspaper.