An harbe 'yan sanda 7 a abuja


Wasu 'yan bindiga da ba'a san ko suwaye ba sun hallaka 'yan sanda 7 har lahira a poloce post, galadimawa dake kan hanyar filin saukar jirgin sama a birnin tarayya abuja nigeria.

An farmaki rayuwakan 'yan sandan ne alokacinda suke bakin aiki yayinda su 'yan bindigar suka zo wucewa da mota su kuma 'yan sandan suka tsayar dasu akan lallai sai sun bincika motar tasu.

Mai magana da yawun 'yan sanda a nigeria DCP jimoh moshood ya bayyanawa manema labarai cewa ba yanzu ne kadai aka fara kai farmaki kan jamian tsaron ba. Ko a kwanakin baya an kashe 'yan sanda biyu a abuja yayinda suke bakin aiki. Ya kum kara da cewa a shirye suke su yaki dukkan wanda ya kawo barazana a zaman lafiyar 'yan kasarnan bare har ya hallaka jamian dake kokarin wanzarda tsaron,  Lallai hakan babban laifi ne kuma sunanan suna bincike duk wanda aka kama da hannu a kisan 'yan sanda to fa hukumar bazata kyaleshi ba.

'Yan bindigar dai wadanda baa san suwaye ba basu bar abin haka ba saida sukayi awob gaba da bindigar daya daga cikin jamian tsaron.