Babbar kotun nigeria wato (Fedaral high court) dake abuja ta bayarda belin tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara a fannin tsaro SAMBO DASUKI wanda ake zargi da dulmuyarda wasu makudan kudade da aka ware kan shaanin tsaro azamanin tsohon shugaba GOODLUCK JONATHAN.
Kotun wacce take zaune a abuja ta bada belin dasuki ne akan tarar naira milyan 200 kuma kotun ta shaidawa manema labarai cewa cigaba da rike SAMBO DASUKI batareda sharia ba ya sabawa kundin tsarin kasar nigeria wanda yabawa wanda ake zargi damar zama batareda tsangwama ba har sai anyi sharia an yanke hukunci.
Idan baku manta ba an kama sambo dasuki ne tun shekarar 2016 ana kuma zarginsa ne da hannu a badakalar kudadenda aka ware domin yaki da ta'addanci musamman a yankun da ake fama da rikice rikice kamar borno, yobe, adamawa da sauran jihohi.
JAMAA NA CIGABA DA TOFA ALBARKACIN BAKINSU KAN WANNAN ALAMARI MUSAMMAN A KAFAFAFEN SADA ZUMUNTAR FACEBOOK, TWITTER, da sauransu.

