Dan wasan kwallo kafan Nigeria Ahmed Musa yayi nasarar zama na 8 a jerin mutane da aka zabi kwallonsu matsayin wacce tafi burgewa a wasan cin kofin duniya.
Ahmed Musa ya bayyana farincikinsa akan wannan nasara dukda cewa bai samu nasarar zama na 1 ba a gasar inda aka sanarda dan wasan kasar Fransa wato "Pavard" shine zakaran gasar kofin duniya.
Ahmed, Ya kuma yabawa masoyansa a shafinsa na #Instagram ya bayyana cewa wannan nasara batashi bace ta masoyansa ce wadanda suke nuna goyon baya gareshi har yakai wannan matsayi kuma hakan zai taimaka masa wajen samu wasu nasarori a nan gaba.
Kwallon Ahmed Musa ta zama ta takwas ne acikin kwallaye 169 na duniya.
Dubban 'yan nigeria a shafukan sada zumunta suketa taya gwanin nasu murna da kuma fatan alkhairi.