Adam A Zango ya nuna farincikinsa gameda kyautar wacce ya kira da wani rabo daga ubangiji ne yabashi ba ikonsa ba, a turance ya rubuta " Its not my power but the power of Allah. Thank you GOD.
Shahraren dan wasan yayita dora hotuna mabanbanta a ranarda suka kaiwa gomnan jihar katsina ziyara tareda abokansa BABAN CHINEDU da kuma amininsa DAUDA KAHUTU RARARA wanda ana ganin duk wani taku da zaiyi a siyasance tareda Adam Zango yake takawa.
A ranar da suka kai ziyarar sun kwashe awanni suna tattaunawa da gomna AMINU BELLO MASARI kuma dama sanannen abu ne yadda gomnan yake baiwa wadannan mawaka kudade. Idan baku manta ba ya taba ware makudan kudade ga mawakan domin su tayashi murnan cin nasarar zabensa a shekarar 2015.
Jarumi ADAM A ZANGO bai fadi takamaiman wanda yabashi kyautar ba saidai alamu daya nuna cewa gidan gomnatin jihar Katsina aka samu wannan babban rabo.
Masu tofa albarkacin bakinsu suna kan tofawa musamman yan asalin jihar katsina dayawa suna ganin wannan kyauta da gomnan keyi kamar wani almubazzaranci da kudin gomnati ne alokacinda talakawa ke kuka kan rashin walwala da ake ciki.
Saidai magoya bayansa suna ganin ba wani abu bane ganin cewa zabe ke karatowa dole zai nemesu saboda siyasarsa.


