Asarar kudi kimanin $16.8 billion babbar asara ce a wajen masu kudin duniya, A wajen masu kudin Africa kuwa kamar rushewar arziki ne ko talauchewa.
Matashin mai kudi kuma mai kamfanin facebook Mark Zuckerberg yayi asarar wasu makudan kudade da suka kai kimamin $16 billion a ranar laraba 25-07-2018 sakamakon tsayawar shigar kudaden kafafen sadarwa daya samu.
Cikin sa'o'i 2 kachal Mark yayi asarar wadannan kudade wanda masu sharhi suka ce inda asarar taci gaba daga laraba zuwa ranar alhamis da tayi sanadin saukar daga matsayin mai kudi na 3 a duniya.
A ranar 9 ga watan july yawan arzikin Aliko Dangote wanda yafi kowa arziki a Africa bai wuce $12.3 billion bayan shima ya tafka wata asara arzikinsa ya sauka daga lissafinda akayi $12.8 billion a ranar 21 watan May, 2018.
An ruwaito cewa wannan asarar da Mark Zuckerberg yayi bata wuce kashi 5 cikin 100 na arzikinsa.

