Sen. Rabiu musa kwankwaso ya kasance daya daga cikin manyan 'yan siyasar nigeria ne tun bayan gama waadinsa na gomnan jihar kano wanda ake ganin tun kafuwar jihar baa taba samun gomna da yayi aiki a jihar kamarsa ba.
Rikicinda ake tsakanin sen. Kwankwaso da Ganduje yana daga sanadiyyar raguwar farin jinin kwankwaso saboda yadda takaddama ke yawan aukuwa tsakaninsu.
Ga kadan daga abubuwanda suka rage tasirin siyasarsa acikin watannin nan.
1. Tun hawansa senata yafi maida hankalinsa akan siyasarsa fiyeda kujerar senata da yake rike daita.
2. Ya daga hankalinsa akan sai ya samu mulkin nigeria kota halin 'ka'ka.
3. Mabiyansa kullum cikin sukar shugaba buhari suke musamman a social media.
4. Baiyi wani aikin azo agani ba a matsayin senata mai wakiltar kano ta tsakiya.
5. Kushe auren diyar gomna ganduje da yayi a watannin baya.
6. Saka rigar adawa da buhari da yayi bayan fage kafin ya bayyana a fili.
7. Yawan sa'insa da yakeyi da abokan hamayya musamman a jiharsa har takai bazai iya shigowa ba'ayi tarzoma ba.
8. Rashin biyayyarsa ga shugabannin jamiyya da kuma dattawa wadanda ke gaba dashi.
9. Mafiyan yawan mabiya kwankwaso matasa ne kuma basu ganin kowa da kima bayan maigidansu.
10. Akidarsa ta kwankwasiyya wacce tazama kamar jamiyya da kuma jan kaya da mabiyansa ke kakabawa kansu wanda hakan kamar wani ci bayane ga tsarin 'yancin raayi.

