KUNGIYAR KWADAGO TAYI ZANGA ZANGA A KADUNA

Kalli yadda kungiyar kwadagon Najeriya (NLC) ta gudanar da zanga-zangar adawa da korar ma'aikatan da gwamnatin jihar Kaduna ta yi.


 An dade ana takun-saka tsakanin gwamantin jihar Kaduna da kungiyar kwadagon Najeriya An fara samun matsalar ce tun bayan gwamnatin Nasir Ahmed El-Rufai ta bayar da sanarwar cewar za ta kori malaman makarantar firamare 22,000 da suka fadi jarabawar 'yan makarantar firamari Kungiyar kwadagon Najeriya ta ce gwamnatin El-Rufai ta kori ma'aikata kimanin 36,000 ciki har da malaman makarantun firamari 22,000 din Ma'aikatan dai suna ganin korar ma'aikan da gwamnatin ta yi an yi ta ne ba a bisa ka'ida ba Ita kuwa gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta dauki matakin korar malaman makarantin firamarin ne domin kare hakkin 'yan talakawa da suke zuwa makarantin gwamnati Kafin ma'aikatan su fito wannan zanga-zangar dai an yi ta fargabar cewar za a hana su fitowa Wannan ne ma ya sa kungiyar kwadagon Najeriya ta fitar da wata sanarwa inda ta gargadi gwamnatin jihar cewa kada ta yi kokarin hana ma'aikatan jihar 'yancin zanga-zanga da dokar kasa ta ba su A ranar Alhamis dai ma'aikata sun fito zanga-zangar a birnin Kaduna Abin tsayawa a gani shi ne in kwalliya za ta biya kudin sabulu Tura wannan labari

#reports via www.bbchausa.com